Nigerian news All categories All tags
Rikicin APC a Kaduna ya kara karfi yayinda wani babban jigo ya yi murabus

Rikicin APC a Kaduna ya kara karfi yayinda wani babban jigo ya yi murabus

Rikicin cikin gida ya sake tunkaro jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kaduna, yayinda manyan mambobin jam’iyyar ke sake sauya sheka daga jam’iyyar.

Hakan ya biyo bayan zargin da suke yi na cewa masu tafiyar da jam’iyyar a jihar basu da kwarewa.

Yan kwanaki kadan baya, wani tsohon dan takarar gwamna a jam’iyyar, Isa Ashiru Kudan ya sauya sheka zuwa jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) sannan a yanzu wani babban jigon jam’iyyar a jihar, Alhaji Lawal Adamu Usman, wanda aka fi sani da Mr LA ya yi murabus.

Rikicin APC a Kaduna ya kara karfi yayinda wani babban jigo ya yi murabus

Rikicin APC a Kaduna ya kara karfi yayinda wani babban jigo ya yi murabus

Usman, wanda ya kasance daga cikin ma’asassan jam’iyyar a Kaduna ya bayyana rashin yiwa yan jam’iyya adalci a matsayin dalilin san a basu fili, da kuma dakatar da yan jam’iyya ba tare da hujja ba a matsayin dalilinsa na barin jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Ango Abdullahi ya hadu da Obasanjo kan zaben 2019 da kashe-kashe

A takardan murabus da ya aikewa shugaban APC na Unguwan Dosa dake karamar hukumar arewacin Kaduna, mazabarsa da kuma Gwamna Nasir El-Rufai, shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole, shugaban jam’iyyar, Asiwaju Bola Tinubu da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari, Usman yace barinsa jam’iyyar APC shine hukunci guda da zai magance rikice-rikice da dama dake jam’iyyar a jihar.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Makarfi ya ce babu laifi don an sake fasalin lamuran Najeriya idan dai har an sabawa ginshikin hakan.

Dan takarar shugaban kasar karkashin lemar PDP yace akwai bukatar sabonta lamuran hukumomin gwamnati wadanda suka hada da hukumomin tsaro domin bautawaa yan Najeriya ba wai shugabanni ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel