Nigerian news All categories All tags
Zaben 2019: Bafarawa ya bayyana kudirinsa na takarar sugabancin kasa

Zaben 2019: Bafarawa ya bayyana kudirinsa na takarar sugabancin kasa

Wani tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya kaddamar da kudirinsa na tsayawa takarar shugabancin kasa a zaben 2019 karkashin lemar Peoples Democratic Party (PDP).

A wata hira jim kadan bayan kaddamar da kudirinsa a gidansa dake Sokoto a karshen mako, Bafarawa yayi ikirarin cewa shi ne ya kawo shugaban kasa Muhammadu Buhari cikin harkar siyasa.

“Siyasa aikina ne, ni dan siyasa ne na asali na shafe sama da karni hudu,” inji shi.

Zaben 2019: Bafarawa ya bayyana kudirinsa na takarar sugabancin kasa

Zaben 2019: Bafarawa ya bayyana kudirinsa na takarar sugabancin kasa

Bafarawa yace: “Shugaban kasa Buhari dalibi na ne, ni na kawo shi harkar siyasa. Ni na bashi tikitin takara lokacin da nike shugaban jam’iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP). Don haka na san yadda zan tafiyar da lamuran kasar da jam’iyyar.”

KU KARANTA KUMA: Buhari ya tausayawa wadanda tashin gas ya cika da su a Kaduna

Bafarawa, wanda ya taba takarar neman kujerar shugaban kasa a Democratic Peoples Party (DPP), yace matsalar Najeriya shine barin yan siyasan da basu kwareba wajen takarar gwamnatin dimokradiyya.

A baya Legit.ng ta rahoto Rikicin cikin gida ya sake tunkaro jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kaduna, yayinda manyan mambobin jam’iyyar ke sake sauya sheka daga jam’iyyar.

Hakan ya biyo bayan zargin da suke yi na cewa masu tafiyar da jam’iyyar a jihar basu da kwarewa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel