Nigerian news All categories All tags
Ango Abdullahi ya hadu da Obasanjo kan zaben 2019 da kashe-kashe

Ango Abdullahi ya hadu da Obasanjo kan zaben 2019 da kashe-kashe

Kakakin kungiyar dattawan arewa, Farfesa Ango Abdullahi ya hadu da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a gidansa dake Abeokuta, jihar Ogun, domin shirya manufofin zaben shugabancin kasa da za’ayi a 2019.

An gudanar da ganawa tsakanin Ango Abdullahi da Obasanjo ne domin tsayar da Magana guda kan dan takara guda, wata majiya ta sanar da jaridar Punch a ranar Lahadi.

An tattaro cewa ganawar wanda ya samu halartan wasu dattawan arewa biyu, ya kasance domin yarjejeniya kan dan takarar arewa da ya kamata a tsayar wanda zai samu cikakken goyon baya daga dukkanin yankunan kasar a zaben 2019.

Ango Abdullahi ya hadu da Obasanjo kan zaben 2019 da kashe-kashe

Ango Abdullahi ya hadu da Obasanjo kan zaben 2019 da kashe-kashe

An tattaro cewa ganawar na daga cikin yunkurin da ake yin a ada dattawan yankunan kasar guda shida domin gabatar da alkibla guda a zaben 2019.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya tausayawa wadanda tashin gas ya cika da su a Kaduna

Bincike ya kuma nuna cewa ganawar zai tattauna kan mafita ga matsalolin tsaro a kasar.

Sun tattauna kan makomar kasar da kuma son ganin an tsayar da wani dan takara baya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel