Nigerian news All categories All tags
Buhari ya tausayawa wadanda tashin gas ya cika da su a Kaduna

Buhari ya tausayawa wadanda tashin gas ya cika da su a Kaduna

Sakon shugaban kasar na kunshe ne a wata sanarwa daga babban hadiminsa, Mallam Garba Shehu, a Abuja a ranar Lahadi.

Shugaban kasar yace yana jin radadinsu a wannan mawuyacin lokaci, da kuma lura da asarar tattalin arziki wanda yan Najeriya masu kwazo suka gina don ganin sun rayu cikin kwadago na gaskiya.

Ya kara da cewa: “A matsayina na mutum, ina sane da asarar da wannan hatsari ya janyo a rayuwar wadannan yan Najeriya masu kwazo.”

Buhari ya tausayawa wadanda tashin gas ya cika da su a Kaduna

Buhari ya tausayawa wadanda tashin gas ya cika da su a Kaduna

Shugaban kasar ya shawarci yan Najeriya da su mayar da hankali sosai wajen kula da bin matakan da suka dace a haraban kasuwancinsu.

A cewarsa, mayar da hankali wajen kula da matakan zai taimaka matuka wajen kore duk wata annoba da zata taso.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Yan sanda suna zanga-zanga a Maiduguri

A baya mun ji cewa a yammacin ranar Asabar gas ya tashi inda ya kona shaguna 14 da wani dakin hada magunguna inda wani mutum daya ya ji rauni a hanyar Ibrahim Taiwo Road dake unguwar Abeokuta a Kaduna.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel