Nigerian news All categories All tags
2019: Dole a samu dan takara daga jihohin nan na arewa 3 idan ana son kayar da Buhari - Kwankwaso

2019: Dole a samu dan takara daga jihohin nan na arewa 3 idan ana son kayar da Buhari - Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya bayyana cewar a shirye yake ya koma tsohuwar jam'iyyarsa ta PDP tare da bayyana sha'awarsa ta yiwa jam'iyyar takarar shugabancin kasa a zaben 2019.

Da yake bayyana cancanta a matsayin dan takarar shugabancin kasa a karkashin jam'iyyar ta PDP, Kwankwaso ya bayyana cewar, dole a tsayar da dan takara shugaban kasa daga jihohin Kano, Kaduna, ko Katsina matukar ana son kayar da shugaba Buhari a zaben 2019.

Kwankwaso ya bugi kirjin cewar shine ya taimaka Buhari a zaben 2015 har ya samu kuri'u miliyan 1.9m a jihar Kano. Kazalika ya bayyana cewar saboda shi jama'a suka zabi gwamna Abdullahi Umar Ganduje a Kano.

2019: Dole a samu dan takara daga jihohin nan na arewa 3 idan ana son kayar da Buhari - Kwankwaso

Rabi'u Musa Kwankwaso

Wadannan kalamai na Kwankwaso da kuma yadda ya ki halartar taron zaben shugabannin APC na kasa, ya tabbatar da cewar baya tare da jam'iyyar.

A satin da ya wuce ne Kwankwaso ya ziyarci Atiku kafin daga bisani ya ziyarci gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose, a fadar gwamnatin jihar dake Ado Ekiti.

DUBA WADANNAN: 2019: Jerin tsofin janar-janar na soji dake kulle-kullen kayar da Buhari zabe

Jiga-jigan 'yan jam'iyyar PDP daga arewacin Najeriya na cigaba da nuna sha'awar yiwa jam'iyyar takarar a zaben shekarar 2019. Daga cikinsu akwai tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Makarfi, gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, da sauran su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel