Harkar siyasa: An yi kira a fatattaki ‘Yan nPDP daga Jam’iyyar APC

Harkar siyasa: An yi kira a fatattaki ‘Yan nPDP daga Jam’iyyar APC

Cham Faliya Sharon wani Marubuci game da harkokin siyasar Najeriya ya tofa albarkacin sa game da batun rikicin Jam’iyyar APC inda wasu tsirarru da ke karkashin lemar nPDP ke barazana ga Jam’iyyar.

Harkar siyasa: An yi kira a fatattaki ‘Yan nPDP daga Jam’iyyar APC

Wasu na kira a kori su Kwankwaso daga Jam’iyyar APC

Mista Cham Faliya Sharon a wani rubutu da yayi a Jaridar Daily Trust ya nemi Jam’iyyar APC ta jefar da kwallon mangwaro ta huta da kuda. Marubucin dai yace ‘Yan nPDP da ba su iya tsinana komai na nema su zama Ala-kai-kai a APC.

Faliya Sharon yace babu dalilin da za a biyewa bukatun ‘Yan nPDP wanda a cewar sa su ka hada da watsi da shari’ar Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki wanda yace ya yaudari Jam’iyyar sa ta APC ta hada-kai da ‘Yan adawa na PDP.

KU KARANTA: Saura kiris ‘Yan adawa su sa hannun yi wa Shugaba Buhari rubdugu

‘Yan nPDP din dai su na kukan cewa ba a yi da su a Jam’iyyar APC don haka su ka nemi su gana da Shugaban kasa Buhari. Faliya Charon yace su kan su Bukola Saraki da Yakubu Dogara sun maida ‘Yan APC a Majalisa saniyar-ware.

Marubucin kuma ya zargi tsohon Gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso da kokarin nunawa Gwamna mai ci Abdullahi Ganduje iko a wajen mulkin Jihar. Faliya Sharon yace lamarin na ‘Yan nPDP na nema ya wuce gona da iri don haka a taka masu burki.

Kun ji labari dai da alamu tsohon Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso yana neman yayi takarar Shugaban Kasa a zaben 2019. Sai dai hakan na iya masa wuya sosai saboda wasu dalilai da masana harkar siyasar kasar su ka zayyano.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel