Nigerian news All categories All tags
Yanzu-yanzu: Atiku ya shiga ganawar sirri da IBB

Yanzu-yanzu: Atiku ya shiga ganawar sirri da IBB

Tsohon mataimakin shugaban kasan Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, yana cikin ganawar sirri da tsohon shugaban kasa, Ibrahim Badamasi Babangida, IBB, a katafaren gidansa da ke Hilltop Minna, jihar Neja. Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Majiyar ta kara da cewa ana kyautata zaton cewa ganawar na da alaka da niyyar takaran shugaban kasan Atiku Abubakar yayinda zaben shekarar 2019 na gabatowa.

Atiku ya isa gidan IBB daga filin jirgin saman gari Minna misalin karfe 12:35pm inda suka tattauna da tsohon shugaban kasa na tsawon kimani sa'ao'i 4.

KU KARANTA: Yan sanda suna zanga-zanga a Maiduguri

Duk da cewan ba'a samu bayanai abubuwan da suka tattauna ba a ganawar ba saboda na hana manema labarai shiga gidan Babangida, majiyoyi sun bayyana cewa ziyararsa na da alaka da takaran zaben 2019.

Yayinda suke ganawar, masoya Atiku sun cika wajen gidan Babangida amma abin mamaki shine da ya fito bai sauraresu ba, innama shiga motarsa yayi ya tafi filin jirgin sama kuma ya tashi misalin karfe 3:45.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel