‘Yan Najeriya ba su yi na’am da matakin da Gwamnatin Buhari ta dauka na rabawa Talakawa dukiyar sata ba

‘Yan Najeriya ba su yi na’am da matakin da Gwamnatin Buhari ta dauka na rabawa Talakawa dukiyar sata ba

Mun fahimci cewa ‘Yan Najeriya da-dama ba su goyi bayan matakin da Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta dauka na rabawa Talakawan Kasar kudi daga cikin dukiyar da tsohon Shugaban kasa Sani Abacha ya sace ba.

‘Yan Najeriya ba su yi na’am da matakin da Gwamnatin Buhari ta dauka na rabawa Talakawa dukiyar sata ba

Za a rabawa Talakawa kudin da aka sace a lokacin Abacha

Sanatan APC Shehu Sani yana cikin wadanda su ka nuna rashin amincewar su game da wannan shawara da Gwamnatin Tarayyar Kasar ta yanke. Gwamnatin Buhari tace za ta kashe Dala Miliyan 322 da aka dawowa Kasar ne kan Talakawan ta.

Shehu Sani wanda shi ke wakiltar Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattawa yace zai fi kyau Shugaba Buhari ya yi wa kasa aiki ne da wannan kudi yadda kowa zai iya ganewa idanun sa ba wai ace za a zabi wasu Talakawa a rika ba wannan kudi ba.

KU KARANTA: Sanatan Kaduna ya ba Magoya bayan Buhari shawara

‘Dan Majalisar na APC ya nuna cewa ba zai yiwu ace Gwamnatin Tarayya za ta iya rabawa Talakawa wannan kudi ba illa ma dai kawai Gwamnoni da Sanatoci da na-kusa da Shugaban kasa ne za su bada sunayen wadanda za a ba wannan kudi.

Kwanakin baya ne mu ka ji labari daga bakin wani babban Jami’i na Gwamnatin Buhari dai yace za ta kashe wadannan kudi ne ta tsarin da ta ke da shin a CCT inda ake rabawa mutum sama da 300, 000 a Jihohi 19 na kasar N5000 kowane wata.

Jihohin da ake raba wannan kudi sun hada da Kogi, Ekiti, Osun, Oyo, Kwara, Bauchi, Gombe, Jigawa, Benuwe, Taraba, Adamawa, Kano, Katsina, Kaduna, Nasarawa, Anambra, Borno da sauran su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel