Nigerian news All categories All tags
Buhari da Osinbajo sun halarci Jana'izar Mahaifiyar Fasto Bakare a Birnin Abeokuta

Buhari da Osinbajo sun halarci Jana'izar Mahaifiyar Fasto Bakare a Birnin Abeokuta

A ranar Asabar din da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da Mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo, suka halarci jana'izar mahaifiyar Fasto Tunde Bakare, Madam Abigail Bakare.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito, Ministar Kudi Misis Kemi Adeosun, ita ta wakilci shugaba Buhari a jana'izar da aka gudanar a cocin Victory Life Bible Church dake yankin Ajebo na birnin Abeokuta a jihar Ogun.

A yayin gabatar da hudubar jana'izar, babban Fasto Lawrence Achumede, ya bayyana cewa Marigayiya Abigail ta kasance mai kulawa da tsayuwa kan tarbiya.

Buhari da Osinbajo sun halarci Jana'izar Mahaifiyar Fasto Bakare a Birnin Abeokuta

Buhari da Osinbajo sun halarci Jana'izar Mahaifiyar Fasto Bakare a Birnin Abeokuta

A yayin godiya mahalarta jana'izar Mahaifiyar sa, Fasto Bakare ya bayyana cewa zai yi matukar rashi da kewar mahaifiyar sa sakamakon rawar da taka a rayuwar sa.

DUBA WANNAN: Ababe 5 da ya kamata ku sani game da shirin Fim din da gwamnan jihar Bauchi zai bayyana a ciki

Legit.ng ta fahimci cewa, shugaba Buhari bai samu halartar jana'izar ba sakamakon ziyarar aiki da tafi kasar Mauritania a ranar Asabar din da ta gabata.

Sauran jiga-jigai da suka halarci ta'aziyyar sun hadar da, Gwamna Ibikunle Amosun tare da matar sa Olofunso Ogbeni, Rauf Aregbesola na jihar Ogun, Bola Ahmed Tinubu da tsaffin gwamnonin jihar Ogun, Cif Olusegun Osoba da Cif Gbenga Daniel.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel