Nigerian news All categories All tags
‘Yan Boko Haram sun kai hari sansanin ‘yan gudun hijira mutum 4 sun hallaka

‘Yan Boko Haram sun kai hari sansanin ‘yan gudun hijira mutum 4 sun hallaka

- Sojoji da 'yan ta'addan Boko Haram sunyi musayar wuta

- Jami'an tsaro biyu sun rasu bayan bata kashin awa guda

Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa a ranar a jiya Asabar mayakan Boko Haram su ka kashe wasu 'yan gudunara hijira guda hudu a sansanin 'yan gudun hijira da ke garin Banki na jihar Borno wacce ke fama da rikicin na Boko Haram.

‘Yan Boko Haram sun kai hari sansanin ‘yan gudun hijira mutum 4 sun hallaka

‘Yan Boko Haram sun kai hari sansanin ‘yan gudun hijira mutum 4 sun hallaka

Mayakan sun shiga sansanin cikin daren Juma'a akan Babura inda su ka budewa yan gudun hijirar wuta.

Karar harbin ce ta janyo hankalin jami'an Sojoji da na yan sanda wanda su ke wajen sansanin na yan gudun hijirar.

KU KARANTA: Wayyo abin tausayi: Mutane 31 sun jikkata yayin da 9 suka kone a wani hadari a hanyar Kaduna

Inda daga nan su ka yi musayar wuta ta kimanin Sa'a guda tsakaninsu da maharan, Wanda hakan ya kawo jikkatar jami'an soji guda biyu, in ji wani jami'in soji da ya bukaci a sakaye sunansa. Kamar yadda jiridar Vanguard ta rawaito.

Kimanin yan gudun hijira 45,000 ke neman mafaka a sansanin na yan gudun hijira da ke garin banki, mai nisan kilomita 130 daga cikin birnin Maidugurin jihar Borno.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel