Wayyo abin tausayi: Mutane 31 sun jikkata yayin da 9 suka kone a wani hadari a hanyar Kaduna

Wayyo abin tausayi: Mutane 31 sun jikkata yayin da 9 suka kone a wani hadari a hanyar Kaduna

- A ƙalla mutane goma ne suka rasu akan babban titin Kaduna zuwa Kano a safiyar yau ranar Lahadin nan

- Sannan karin wata mata ta rasa ranta bayan an kaita asibiti sakamakon hatsarin

Kamfanin dillacin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa hatsarin ya faru ne da misalin karfe 5:30am na safe a yau Lahadi a daidai kusa da Makarantar Nuhu Bamalli dake Zariya.

Wayyo abin tausayi: Mutane 31 sun jikkata yayin da 9 suka kone a wani hadari a hanyar Kaduna

Wayyo abin tausayi: Mutane 31 sun jikkata yayin da 9 suka kone a wani hadari a hanyar Kaduna

Shugaban wayar da kan al'umma na hukumar kiyaye hadura ta jihar Kaduna, Malam Yahaya Idris ya tabbatar da faruwar lamarin.

Yahaya ya ce Hatsarin ya auku ne a tsakanin abubuwan hawa guda uku, babbar mota kirar Luxury mai lamba GDD361YE, sai ƙananan motoci guda biyu masu lambar SGR57XA da kuma LND246XE.

"A cikin abubuwan hawan guda uku akwai aƙalla mutane 48 wanda mutane 9 sun ƙone har lahira sai mace 1 da ta rasu a asibiti, sai kuma mutane 31 da suka jikkata".

KU KARANTA: Kaico: Bayan nutsewar wasu yara ukku, ana can ana jimami a Sakkwato

“Direban babbar motar kirar luxury yana asibitin koyarwa na Jami'ar Ahmadu Bello dake Shika, a Zariya yana karbar magani”.

Jami’in kiyaye haduran ya bayyana cewa ragowar mutanen da suka samu raunin suna asibitin koyarwar na jami'ar ta Ahmadu Bello Zariya inda ake cigaba da kula da lafiyarsu, wanda suka rasu kuma an kai gawarsu ma'adanar gawarwaki kafin yan uwansu su zo.

Sannan ya ce "Ya kamata direbobi suke tuƙi cikin nutsuwa, sannan su tabbatar suna da tayoyi masu kyau da ƙarko musamnan a cikin wannan yanayi da ake ciki na damuna, ba wai suke amfani da tayar da ta kwana biyu ba domin hakan ka iya zama sanadiyyar salwantar rayukan jama'a".

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel