Nigerian news All categories All tags
Na fadawa Sarkin Saudiyya a karyar da farashin fetur – Inji Donald Trump

Na fadawa Sarkin Saudiyya a karyar da farashin fetur – Inji Donald Trump

- Farashin ‘danyen man fetur na daf da yin kasa a kasuwar Duniya

- Shugaban Amurka Trump ya nemi Saudi ta karya farashin na mai

Mun samu labari daga kasar waje cewa anasa rai farashin gangar danyen man fetur zai yi kasa a Duniya. Hakan dai zai iya kawowa Najeriya matukar cikas a fannin tattalin arziki.

Na fadawa Sarkin Saudiyya a karyar da farashin fetur – Inji Donald Trump

Shugaban Amurka Trump ya nemi a rage farashin man fetur

Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa bai jin dadin yadda farashin man fetur yayi ‘dan karen tsada a Duniya don haka ya nemi Kasar Saudi ta karya farashin. Trump ya kuma ce Kasar Saudi ta amince da hakan.

KU KARANTA:

Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa matsalar da ake samu daga Kasar Iran da Venezuwala ne ya sa danyen fetur ya kara kudi a kasuwa don haka ya nemi Sarki Salman na Saudi ya kara yawan man da yake hakowa.

Bayan wayar da aka yi tsakanin Shugaban na kasar Amurka da Sarki Salman na Saudiyya, da alamu an ci ma matsaya, kuma Saudi za ta rika tace danyen mai kusan har ganga Miliyan 2 a duk rana ta Allah. Hakan dai zai sa fetur yayi araha.

Donald Trump duk ya bayyana wannan ne a shafin sa na sadarwa na Tuwita. Kusan har yanzu Najeriya dai ta dogara da man fetur ne kuma ba za ta ji dadin saukar farashin ba inda ta ke sa ran kashe kudi har sama da Naira Tiriliyan 9 a bana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel