Nigerian news All categories All tags
Akwai matsala a Najeriya don haka mu ma daina yaudarar kan mu – Gwamna Tambuwal

Akwai matsala a Najeriya don haka mu ma daina yaudarar kan mu – Gwamna Tambuwal

Mun samu labari cewa Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya fito ya fadawa jama’a hakikanin gaskiya game da lamarin kasar nan inda yace dole Shugabanni su rike nauyin da ke kan su.

Akwai matsala a Najeriya don haka mu ma daina yaudarar kan mu – Gwamna Tambuwal

Gwamna Tambuwal yace abubuwa sun cabe a kasar nan

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Gwamnan na Jihar Sokoto Aminu Tambuwal ya bayyana akwai babban matsala a Kasar kuma dole a tashi tsaye domin maganin wadannan matsaloli. Gwamnan yayi wannan jawabi ne wajen wani taro na NUJ.

A wajen taron na ‘Yan jaridar kasar da aka yi a Garin Sokoto, Gwamnan yayi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi wani abu game da yadda Hafsun Sojojin Kasar ke aiki ya kuma kara da cewa dole a kawo wasu masu tunani dabam.

KU KARANTA: Kwankwaso yace idan aka ba shi dama sai ya buge Buhari a 2019

Tambuwal ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta kirkiro ‘Yan Sanda na Jihohi domin magance matsalar tsaro a Kasar. Gwamnan ya koka da cewa wani lokaci Kwamishinan ‘Yan Sanda ba su daukar wayar Gwamnoni lokacin da ake bukatar su.

A wajen taron ma dai tsohon Gwamnan Sokoto kuma Sanatan Jihar a yanzu watau Aliyu Magatakarda Wammako yayi kira ga ‘Yan jarida su rika gaskiya a aikin su. Isa Galadanci ne ya wakilci Sanatan a wajen taron da aka yi kamar yadda mu ka ji.

Kwanaki kun ji cewa Sufeta na Sojin Najeriya ya aika Runduna ta musamman zuwa Garuruwan Barkin Ladi da kuma Kudancin Jos inda rikici ya ci sama da mutane 100 a makon da ya wuce.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel