Nigerian news All categories All tags
Manyan ayyukan da ke gaban Adams Oshiomhole domin dawo da martabar Jam’iyyar

Manyan ayyukan da ke gaban Adams Oshiomhole domin dawo da martabar Jam’iyyar

A makon jiya ne Kwamared Adams Oshiomhole ya zama sabon Shugaban Jam’iyyar APC mai mulki. Jaridar Daiy Trust ta kasar nan ta kawo wasu manyan ayyuka da ke gaban sabon Shugaban na Jam’iyyar APC kafin zabe mai zuwa.

Manyan ayyukan da ke gaban Adams Oshiomhole domin dawo da martabar Jam’iyyar

Tsohon Gwamnan Edo Adams Oshiomhole ya zama Shugaban Jam’iyyar APC

Daga cikin abubuwan da ake tunani Adams Oshimhole zai fara tinkara ga su kamar haka:

1. Rikicin Majalisa da Fadar Shugaban Kasa

Akwai kwantaciyyar rikici tsakanin fadar Shugaban kasa da kuma Majalisar Dattawa da ta Wakilai. Hakan dai ya jawo matsala wajen tantance wasu da Shugaba Buhari ya ba mukamai da kuma harkar kasafin kudin kasar. Don haka dole a kawo karshen rikicin domin Gwamnati ta zauna lafiya.

KU KARANTA: Gwamnan Bauchi zai fito a wani fim a Najeriya

2. Rikicin cikin gida a Kano da Kaduna

Ana rikici a cikin Jam’iyyar APC a Jihohi da dama musamman a Kano inda Rabiu Kwankwaso ya samu sabani da tsohon Mataimakin Abdullahi Ganduje. Haka kuma a Kaduna ana rikici tsakanin Nasir El-Rufai da duka Sanatocin sa wanda hakan na iya kawowa Shugaba Buhari matsala a 2019.

3. Fara shirin zaben fitar da gwani

A watanni masu zuwa ne Jam’iyyar APC za ta ba ‘Yan takarar ta na zaben 2019 tikiti. Idan dai ba a bi tsari ba wajen zaben fitar da gwani ba za a samu sabon rikici. Dole a bi doka wajen bada tutar Jam’iyyar idan har Oshiomhole yana so Jam’iyyar ta kai labari a 2019.

4. Zaben Gwamnoni a Jihohi Osun da Ekiti

Kwanan nan za ayi zaben sababbin Gwamnoni a Jihohin Ekiti da kuma Osun. A baya PDP ta karbe Sanata daga Osun inda kuma a 2014 Jam’iyyar PDP ta tika APC da kasa a Jihar Ekiti. Zaben da ke gabatowa za su nunawa APC yadda ya kamata ta wanke allon ta a 2019.

5. Matsalar rashin kudi a Jam'iyya

Jam’iyyar APC na kukan cewa ba ta da kudi domin gudanar da ayyukan Jam’iyya. Dole Adams Oshimhole ya sa yadda zai nemowa Jam’iyyar mai mulki kudin gudanarwa. Wasu ma na cewa APC na bukatar wani sabon Hedikwata domin na yanzu bai da girma.

Dazu kun ji labari cewa bisa dukkan alamu dai tsohon Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso yana neman yayi takarar Shugaban Kasa a zaben 2019 kuma zai gamu da cikas da dama.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel