Nigerian news All categories All tags
2019: Jam’iyyun adawa sun hada-kai za su yi wa APC taron dangi

2019: Jam’iyyun adawa sun hada-kai za su yi wa APC taron dangi

Mun samu labari daga Jaridar Tribune cewa manyan Jam’iyyun adawan kasar nan sun gama shirye-shiryen yadda za su tika Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kasa a zabe mai zuwa na 2019.

2019: Jam’iyyun adawa sun hada-kai za su yi wa APC taron dangi

Jam'iyyun adawa za su hada-karfi da karfe su yi wa Buhari illa

Kusan dai ba shakka Jam’iyyar APC za ta tsaida Shugaba Buhari ne a matsayin ‘Dan takarar Shugaban kasa a zaben na 2019 don haka ne Jam’iyyun adawar Kasar kusan 40 sun hada-kai za su yi wa Shugaba Buhari taron dangi.

Labarin da mu ke samu shi ne Jam’iyyar adawa ta PDP da Takwarar ta SDP da LP a ADC da kuma wasu ‘Yan nPDP na daf da sa hannu a wata yarjejeniya inda su ka zari takobin fatattakan Shugaba Buhari daga kujerar Shugaban kasa.

KU KARANTA: Wasu tsofaffin Sojoji na yi wa Buhari kulle-kulle game da 2019

Majiyar ta mu ta bayyana cewa manyan Jam’iyyun sun yi wani taro inda su ka cin ma matsaya cewa dole a yaki Shugaba Buhari a 2019 saboda yadda Najeriya ta samu rabuwar kai da kuma matsaloli ta fannoni da dama a Gwamnatin nan.

Yanzu dai abin da ya rage shi ne a fitar da Jam’iyyar da za ayi amfani da ita a 2019. Kuma a mako mai zuwa ne za ayi wani babban taro a Garin Benuwe inda manyan Kudancin kasar nan da ‘Yan siyasar Arewa ta tsakiya za su sa labule game da 2019.

Kwanaki Tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo wanda ya saba sukar Gwamnatin Buhari ya tofa albarkacin sa game da rikicin Filato inda aka kashe mutane da dama a Garin Jos. Obasanjo yayi wa al’umma jajen abin da ya auku ya nemi a kawo karshen rikicin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel