Nigerian news All categories All tags
Zaɓen jihar Ekiti: Hukumar zaɓe ta ƙasa ba ta raba kayan aiki a wasu ƙananan hukumomi ba

Zaɓen jihar Ekiti: Hukumar zaɓe ta ƙasa ba ta raba kayan aiki a wasu ƙananan hukumomi ba

- Kasa da kwanaki 15 kafin gudanar da zaben gwamna a jihar Ekiti, har yanzu kayan aiki ba su kai wasu wurarenba

- Sai dai 'yan takarar APC da PDP sun tsimma matsaya

- Wani ministan Buhari ne ya ajiye mukaminsa don ya kara da mataimakin gwaman jihar a zaben da za'a gudanar 14 ga watan Yuli

Hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) bata raba kayan zaɓe a ƙananan hukumomi guda goma sha ɗaya ba duk da cewa zaben dan takarar gwamnan jihar yana karatowa wanda za a yi a 14 ga wannan wata da muke.

Zaben Gwamnan Ekiti 2018, INEC ta rarraba kayan aiki

Zaben Gwamnan Ekiti 2018, INEC ta rarraba kayan aiki

Da yake bayyanawa manema labarai a yayin wani taron masu ruwa da tsaki game da harkokin tsaro a jihar kafin zaben Farfesa Abdulganiy Raji yace ya zuwa yanzu babu wasu kayan aiki da suka bayyana a wadancan kananan hukumomi guda goma sha shida.

Taron ya samu wakilci daga bangarorin hukumomin tsaro da suka hada da jami'an tsaro na farin-kaya, hukumar shige da fice, jami'an gidan yari, da sauransu.

A yayin ganawar ya bayyana musu cewa suna sa ran samun kayan aikin zaben kafin ranar da za a gudanar da zaben.

Farfesa Abdulganiy ya bayyana cewa hukumar zabe zata yi wa kowacce jam'iyya adalci a zaben, ta hanyar ƙirga ƙuri'un da aka kaɗa tun daga mazaɓu ba wai lallai sai an zo ofishin zaɓe ba.

"Mun ji dadin taron da muka yi da Jam'iyyun siyasar, inda kowannensu suka nuna goyan baya domin samun sahihin zabe. Kamar yadda muka yi alkawari zamu kasance masu cika alkawari daga bangaren mu domin ganin komai ya tafi yadda ya kamata wajen gudanar da zaben ba tare da an samu korafi ba".

KU KARANTA: Burina na gina coci-Inji wani shugaban yan fashi da makami bayan da ya shiga hannun hukuma

'Yan takarar gwamnan sun bayyana zasu kasance masu ɗa'a da kuma samar da zaman lafiya domin cigaban jihar ta Ekiti.

Dan takarar gwamna a karkashin inuwar Jam'iyyar APC Dakta Kayode Fayemi ya ce hukumomin tsaro sun bamu tabbacin samar sa cikakken tsaron dukiya da kuma rayukan al'umma, sannan ya yi tsokaci game da kashe-kashe da aka samu a baya inda ya nuna goyon bayansa domin tabbatar da zaman lafiya.

Zaben Gwamnan Ekiti 2018, INEC ta rarraba kayan aiki

Zaben Gwamnan Ekiti 2018, INEC ta rarraba kayan aiki

Daga bangaren Jam'iyyar PDP kuwa, dan takararta Kolapo Olusola ya bukaci jama'a da su kasance masu nuna son zaman lafiya a lokacin zabe.

Zaben Gwamnan Ekiti 2018, INEC ta rarraba kayan aiki

Zaben Gwamnan Ekiti 2018, INEC ta rarraba kayan aiki

Sannan yayi kira don kowa ya fito ya yi zaben cikin salama ba tare da tashin hankali ba saboda gwamnatin tarayya ba zata sa musu hannu a cikin zaben ba, inda ya kara da jan hankalin mutane wajen muhimmancin yin zaben.

Shi ma daga bangarensa shugaban rundunar yan sanda ta jihar Ahmed Bello ya bada tabbacin jami'an hukumar suna cigaba da zage damtse wajen ganin komai ya tafi daidai a mazabu yayin zaben da za a gudanar.

Ahmed ya ce, "Dalilin yin wannan taro shi ne mu bayyanawa yan takara yanayin da ake ciki, da kuma irin gudunmawar da zamu bayar a wannan zaben".

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel