Nigerian news All categories All tags
An tsinto gawawwakin Mutane 23 cikin dokar Daji a jihar Zamfara

An tsinto gawawwakin Mutane 23 cikin dokar Daji a jihar Zamfara

Kimanin gawawwakin mutane 23 aka tsinto cikin dokar wani daji dake karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya bayyana.

Ko shakka babu jihar Zamfara ta sha fama da tashin-tashina ta afkuwar hare-haren makiyaya, 'yan fashi da makami da kuma barayin shanu da suka salwantar da rayukan mutane bila adadin gami da asarar dukiya musamman a yankunan karkara dake fadin jihar.

Kamar yadda shafin jaridar ta Daily Trust ya ruwaito, mafi akasarin gawawwakin an yanka maƙogwaron su ne yayin da wasun suka mutu a sakamakon harbin harasashi na bindiga da har yanzu an rasa gane dalilin da ya sanya aka zartar da wannan ta'addanci a kansu.

An tsinto gawawwakin Mutane 23 cikin dokar Daji a jihar Zamfara

An tsinto gawawwakin Mutane 23 cikin dokar Daji a jihar Zamfara

Sai dai wata majiyar rahoton ta bayyana cewa, akwai yiwuwar wannan mutane sun gamu da makasan su ne yayin da suke kan hanyar su ta kaura daga wani yankin zuwa wani yankin.

KARANTA KUMA: Wata Kungiya ta yabawa jami'ar Legas kan bayar da kyautar gwarzon Gwamnoni ga Dankwambo

Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar SP Muhammad Shehu ya bayyana cewa, hukumar 'yan sandan ta samu nasarar tsinto wannan gawawwaki a sakamakon wani rahoto da suka samu na cewar an tsinci gawawwakin cikin wani Daji dake yankin karamar hukumar ta Zurmi.

Legit.ng ta fahimci cewa, hukumar 'yan sandan ta tabbatar da wannan lamari yayin da ta fita cikin gaggawa domin tabbatar da sahihancin wannan rahoto, inda a halin yanzu an fara gudanar da bincike cikin taku domin bankado wadanda suka aikata wannan mummunan ta'addanci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel