Nigerian news All categories All tags
Kwankwaso ya huro wuta, yace shi a PDP zasu kada Buhari a badi

Kwankwaso ya huro wuta, yace shi a PDP zasu kada Buhari a badi

- Ana daf da sake walagigi da zuba katin kartar yadda jiga-jigai zasu kara a zabukan 2019 daga manyan jam'iyyu

- Ya bayyana jam'iyyar PDP a matsayin jam'iyyar da tafi adawa da APC kuma mai karfin kayar da shugaban kasan a zaben mai zuwa, wanda za a yi a watan Fabrairu mai zuwa

- Ya kara da cewa, shine Dan takara mafi cancanta da zai iya rike tutar jam'iyyar kuma yaci zaben shugabancin kasar

Kwankwaso ya huro wuta, yace shi a PDP zasu kada Buhari a badi

Kwankwaso ya huro wuta, yace shi a PDP zasu kada Buhari a badi

Rabiu Musa Kwankwaso, daya daga cikin jiga jigan jam'iyyar APC wanda ke ware kanshi daga jam'iyyar mai mulki, yace za a kada shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019 mai tunkarowa.

Ya bayyana jam'iyyar PDP a matsayin jam'iyyar da tafi adawa da APC kuma mai karfin kayar da shugaban kasan a zaben mai zuwa, wanda za a yi a watan Fabrairu mai zuwa.

Ya kara da cewa, shine Dan takara mafi cancanta da zai iya rike tutar jam'iyyar kuma yaci zaben shugabancin kasar.

Kwankwaso, Sanata ne mai ci a yanzu kuma tsohon gwamnan jihar Kano, yana yawan ikirarin cewa da taimakon shi Buhari ya samu kuri'u miliyan 1.9 a jihar tashi. Ya kuma taimakawa gwamna Umar Ganduje, mataimakin shi a lokacin da ya rike Gwamnatin jihar, cin zaben 2015.

DUBA WANNAN: Ta kashe mijinta kan batun kishiya

Wannan sukar jam'iyyar APC ta fito ne bayan kwanaki kadan bayan da yaki halartar zaben jam'iyyar da akayi a Abuja. Wannan ya faru ne sakamakon fadan da ke tsakanin magoya bayan shi da na gwamna Ganduje, wanda duk haduwar su sai sun raba abin fadi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel