Kaico: Bayan nutsewar wasu yara ukku, ana can ana jimami a Sakkwato

Kaico: Bayan nutsewar wasu yara ukku, ana can ana jimami a Sakkwato

- Labarin yara 3 da ruwa ya ci a ranar 24 ga watan yuni ya firgita mazauna Gumbi, karamar hukumar Wamakko na jihar Sokoto

- Anyi zargin yaran sun shiga guri mai zurfi ne na rafin, wanda a da rijiya ce da mazauna garin ke diban ruwa

- Yaron da ya tsira, Hashimu Sani, yace da kyar ya samu ya fita daga ruwan da yaci abokan shi

Kaico: Bayan nutsewar wasu yara ukku, ana can ana jimami a Sakkwato

Kaico: Bayan nutsewar wasu yara ukku, ana can ana jimami a Sakkwato

Muhammad Sani mai shekaru 12, Muhammad Abdulaziz mai shekaru 12 da Fodiyo mai shekaru 7 suna hanyar su ta zuwa gida tare da wasu yara ukun, bayan sunyi kara.

Sai suka yanke shawarar wanka a wani karamin rafi wanda yake karkashin gada. Hudu daga cikin su suka shiga ruwan, inda biyu suka tsaya kallon su ta saman gadar.

Anyi zargin yaran sun shiga guri mai zurfi ne na rafin, wanda a da rijiya ce da mazauna garin ke diban ruwa.

Yaron da ya tsira, Hashimu Sani, yace da kyar ya samu ya fita daga ruwan da yaci abokan shi.

Kamar yanda majiyar mu ta sanar damu, Sani yace, mahaifiyar daya daga cikin yaran da ruwan yaci, ta aike mu samo mata kara. Da kyar na samu nima na fita daga ruwan.

DUBA WANNAN: Ta kashe mijinta kan batun kishiya

Bayan na fito ne a hanyata ta zuwa gida ne na hadu da wani tsoho na fada mishi abinda ya faru. A take ya bar jakin shi, muka koma rafin, ya shiga ruwan ya fito da gawarwakin biyu dafa ciki. Daga baya aka je aka nemo gawar dayan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel