Nigerian news All categories All tags
Babu Jihar da na fi sha’awa irin Ribas – Inji Paul Arkwright

Babu Jihar da na fi sha’awa irin Ribas – Inji Paul Arkwright

- Jakadan Kasar Ingila da ke Najeriya yace yana jin dadin zama a Jihar Ribas

- Wakilan Kasar na Birtaniya yace akwai sha’anin tsaro a Yankin na Neja-Delta

Mun samu labari cewa kwanaki ne Jakadan Kasar Birtaniya da ke Najeriya watau Paul Arkwright ya bayyana Jihar da ta fi kowace ba shi sha’awa kuma ya fi jin dadin zama cikin ta a kaf fadin Najeriya.

Babu Jihar da na fi sha’awa irin Ribas – Inji Paul Arkwright

Jakadan Birtaniya Paul Arkwright yace Jihar Ribas ta kwanta masa a rai

Jakadan na Birtaniya a Kasar nan Paul Arkwright yace babu Jihar da ta fi ba shi sha’awa irin Ribas da ke Kudancin Najeriya. Arkwright yace a ko yaushe ya bushi iska zai iya kama hanya ya wuce Garin Fatakwal babu wani fargaba.

KU KARANTA: Wani Sarki yace su na bayan Shugaba Buhari a 2019

Kwanan nan ne Gwamna Nywesom Wike ya cika shekaru 3 a kan karagar mulki don haka ya gayyaci Wakilin na Birtaniya da ke Najeriya ya halarci bikin taya sa murna. A wajen taron ne Jakadan ya yabi Jihar Ribas da ke Kudu maso kudu.

Paul Arkwright yace ban da cewa ba ya jin tsoron shiga Fatakwal, Jihar kuma na dauke da dinbin arziki musamman a harkar noma da kimiyya da fasaha da sauran su. Sai dai Jakadan ya nemi ayi maganin matsalar tsaro da ke Yankin.

A Yankin na Neja-Delta dai ana fama da tsageru masu tada kafar-baya. Jakadan yace duk lokacin da aka sace wani Bature, a kan samu labari a Duniya. A wajen bikin dai Gwamna Nyesom Wike ya kaddamar da wasu ayyuka a fadin Jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel