Rana bata karya: Atiku ya yi alkawarin zuwa Amurka

Rana bata karya: Atiku ya yi alkawarin zuwa Amurka

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce a shirye yake ya tafi Amurka muddin jami'an kula da shige da fice na kasar suka amince da takardar izinin neman shiga kasar da ya ke nema.

Mr. Abubakar wanda ya kasance mataimakin shugaban kasa daga 1999 zuwa 2007 bai samu iznin shiga Amurka ba tun bayan da ya sauka mulki.

"Idan Amurka ta bani visa yau, zan dare jirgin sama kama hanya cikin yan kwanaki," Atiku ya fada wa wani mai sharhin siyasa Dele Momodu a hirar da su kayi a farkon wannan makon.

KU KARANTA: 2019: Wadanda PDP zata tsayar da ka iya razana Buhari

Momodu ya na bin dukkan masu neman tsayawa takarar shugabancin Najeriya yana hira da su saboda su al'umma su san manufofin dukkan masu neman tsayawa takarar a shekarar 2019.

A dai 'yan kwanakin nan ne tsohon mataimakin shugaban kasar ya fito ya karyata labarin cewa wata kungiyar masanna masu neman cigaban Afirka sun gayyace zuwa Amurka.

Karyata gayyatar da akayi masa ya sanya mutane sun kara samun shakku kan dalilan da yasa tsohon shugaban kasan ya kasa zuwa kasa mafi bunkasa a duniya na tsawon shekaru masu yawa.

Masu adawa da Atiku Abubakar sun dade suna zargin cewa ya kasa zuwa Amurka ne saboda ana tuhumarsa da aikata laifin rashawa.

Daya daga cikin zargin da ake masa ya shafi wata kwangila da aka bawa kamfanin Amurka mai suna iGate na bunkasa intanet a Najeriya a shekarun 2000. An ce Atiku ya karbi wasu kudade ba bisa ka'ida ba saboda ya taimaki kamfanin Amurkan samun kwangilar.

Kotun Amurka ta daure wani dan siyasa, Williams Jefferson saboda samun shi da hannu cikin badakalar kwangilar da su kayi tare da Atiku. An ce jami'an tsaro sun gano makuden dalolin Amurka a firinjin Jefferson wanda ake kyautata zaton cikin kudaden da aka biya Atiku ne.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel