Nigerian news All categories All tags
Ana yi wa duk wanda ya soki Gwamnatin Buhari tabon sata da rashin gaskiya – Sanata Shehu Sani

Ana yi wa duk wanda ya soki Gwamnatin Buhari tabon sata da rashin gaskiya – Sanata Shehu Sani

Mun samu labari cewa ‘Dan Majalisar da ke wakiltar Kaduna ta tsakiya a karkashin Jam’iyyar APC mai mulki Shehu Sani yayi tir da dabi’ar wasu masoya Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Ana yi wa duk wanda ya soki Gwamnatin Buhari tabon sata da rashin gaskiya – Sanata Shehu Sani

Shehu Sani yace duk wanda ya soki Gwamnatin Buhari sunan sa barawo

Sanata Shehu Sani yace da karfi da yaji yanzu an maida duk wanda ya soki Gwamnatin Shugaban Kasa Buhari barawo ko kuma a saka masa tabon rashin gaskiya ko kuma a rika yi masa kallon wani mutumin kawai makiyin Najeriya.

Kwamared Shehu Sani ya bayyana cewa wadanda su ka sha su ne kurum wadanda su ka dauka cewa Shugaban Kasar ba ya laifi. ‘Dan Majalisar dai yayi wannan jawabi ne a shafin sa na sada zumunta na Tuwita a karshen makon nan.

KU KARANTA: Yadda wani Bawan Allah ya tafi Kasar Rasha a keke domin ya ga Messi

Sanata Sani ya nuna cewa hakan sam bai dace ba domin kuwa wani lokaci dole a samu sabani da bambancin ra’ayi da Gwamnati. A cewar Sanatan na Kaduna dai idan abubuwa su na tafiya a haka dole ba za a rika samun jituwa ba a Kasar.

Har wa yau dai a wani jawabi da Sanatan yayi a shafukan sa na zamani ya wanke hannun Shugaba Buhari daga rikice-rikicen da ke barkewa a Kasar. Sanatan na Kaduna yace amma duk da haka sai Gwamnati ta tashi tsaye domin kare al’umma.

Kwanaki kun ji cewa Jam’iyyar PDP ta zargi APC da kashe makudan kudi har kusan Naira Biliyan 4 wajen babban taron Jam’iyyar mai mulki da aka yi kwanan nan a Birnin Tarayya Abuja.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel