Nigerian news All categories All tags
Wata Kungiya ta yabawa jami'ar Legas kan bayar da kyautar gwarzon Gwamnoni ga Dankwambo

Wata Kungiya ta yabawa jami'ar Legas kan bayar da kyautar gwarzon Gwamnoni ga Dankwambo

Wata kungiyar al'adu da zamantakewa ta jihar Kano, Kano Renaissance Group, ya yabawa hukumar jami'ar Legas dangane da bayar da kyautar gwarzon gwamnoni ga gwamnan jihar Gombe, Dakta Ibrahim Hassan Dankwambo.

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya bayyana, a ranar Asabar din makon da ya gabata jami'ar ta bayar da kyautar gwarzon gwamnonin ga Talban na jihar Gombe.

Wata Kungiya ta yabawa jami'ar Legas kan bayar da kyautar gwarzon Gwamnoni ga Dankwambo

Wata Kungiya ta yabawa jami'ar Legas kan bayar da kyautar gwarzon Gwamnoni ga Dankwambo

Kungiyar cikin wata sanarwar da sa hannnu mukaddashin shugaban ta, Alhaji Sagir Isa, ta bayyana cewa ko shakka babu gwamnan ya cancanci wannan kyauta ta gwarzon gwamnoni da jami'ar jihar Legas ta bai wa gwamna Dankwambo.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari mutum ne Nagari - Sarkin Katsina

Alhaji Isa yake cewa, Dankwambo ne kadai cikin gwamnonin Najeriya ya hade kan al'ummar jihar sa da a halin yanzu suke jin dadi tare da ribatar wannan kokari da ya gudanar.

Kungiyar ta kuma bayyana cewa, Najeriya tana da muradin jagora makamancin gwamna Dankwambo da zai hade kan al'ummar kasar nan wuri guda da zummar tabbatar da ci gaba sabanin aminci da har yanzu bai kai kasar nan ko ina ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel