'Yan Bindiga sun sace Shanu 9, sun kashe mutum 1 a jihar Filato

'Yan Bindiga sun sace Shanu 9, sun kashe mutum 1 a jihar Filato

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito, wasu 'yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kai hari tare da salwantar da rayuwar mutum guda da sace shanu tara a birnin Jos na jihar Filato.

Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, DSP Terna Tyopev, shine ya bayyana hakan a ranar Asabar din da ta gabata yayin ganawa da manema labarai.

Tyopev ya bayyana cewa, wannan shanu da maharan suka yi awon gaba dasu mallakin wani babban Limanin cocin Anglican ne dake birnin Jos, Benjamin Kwashe.

'Yan Bindiga sun sace Shanu 9, sun kashe mutum 1 a jihar Filato

'Yan Bindiga sun sace Shanu 9, sun kashe mutum 1 a jihar Filato

Wannan lamari ya afku ne a kauyen Kangan dake karamar hukumar Jos ta kudu a jihar ta Filato da misalin karfe 7.00 na sanyin safiyar ranar yau ta asabar.

DUBA WANNAN: 'Yan Najeriya dake Haure sun goyi bayan kudirin Atiku na neman kujerar Shugaban Kasa

Legit.ng ta fahimci cewa, a yayin wannan hari ne maharan suka yi awon gaba da shanu tara yayin da suka harbe wani dan Bijilanti, Adamu Dung.

Kakakin ya ci gaba da cewa, an killace gawar wannan mamaci a adakin ajiyar gawa dake asibitin jami'ar Bingham dake garin Jos.

Ya kara da cewa, jami'an tsaro na 'yan sanda tuni sun fara gudanar da bincike kan lamarin domin kakkabo miyagun dake da hannu wajen aikata wannan mummunan ta'addanci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel