Nigerian news All categories All tags
2019: Wadanda PDP zata tsayar da ka iya razana Buhari

2019: Wadanda PDP zata tsayar da ka iya razana Buhari

Wasu masu sharhi kan harkokin siyasa sunyi hasashen cewa mulkin jam'iyyar APC ta kusa kawo karshe, wasu ma suna ganin za'a samu matsala sosai wajen taron kasa na jam'iyyar. Sai dai hakan bai faru ba, yanzu kuma kowa yana sanya idanu ne a zaben 2019.

Hakan yasa Legit.ng Hausa ta kawo muku jerin sunayen wasu mutane da PDP za ta tsayar da zasu iya razana Shugaba Muhammadu Buhari.

1) Atiku Abubakar

Tuni tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana niyyarsa na fitowa takarar zabe a 2019 a karkashin jam'iyyar PDP. Atikun ya dade yana sukar gwamnatin da rashin tabuka wa mutanen Najeriya wani abin arziki tun hawarsu mulki.

2) Ahmed Makarfi

Makarfi ya kwashe shekaru takwas a matsayin gwamna jihar Kaduna kuma daga bisani ya yi shekaru takwas a majalisar dattawa. Ya kuma zama shugaban PDP na rikon kwarya yayin da jam'iyyar ke fama da rikice-rikice.

Shima Sanata Makarfi ya bayyana niyyarsa na fitowa takarar shugabancin kasa a karkashin jam'iyyar PDP.

3) Sule Lamido

Shima tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma daya daga cikin wadanda suka kafa jam'iyyar PDP ya bayyana sha'awar fitowa takarar shugaban kasar a shekarar 2019. Masu sharhi kan siyasa sunyi hasashen akwai yiwuwar tsohon ministan harkokin kasashen wajen ya samu tikitin takara PDP saboda kwarewarsa da gogewarsa a siyasa tare da irin hidimar da ya yi wa jam'iyyar.

4) David Mark

David Mark, tsohon shugaban majalisar dattawa daga jihar Benuwe wanda ya yi shekaru 12 a majalisa. Ya kuma yi gwamnan jihar Neja a zamanin mulkin soja. A lokacin da ya ke shugaban majalisa an samu zaman lafiya da natsuwa saboda irin hikimarsa wajen warware matsaloli.

Duk da cewa Mark bai fito filli ya bayyana cewa yana son fitowa takarar shugabancin kasa ba, majiyar Legit.ng ta gano cewa kungiyoyi da dama musamman daga Arewa ta tsakiya suna ta rubuta wasika inda suke nemansa ya fito takarar.

5. Malam Ibrahim Shekarau

Kamar Lamido da Atiku, shima tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ya sanar da jam'iyyar PDP cewa yana son fitowa takarar shugabancin kasa a shekarar 2018. Mutane da dama suna ganinsa a matsayin dan siyasa ba baya wasa wajen neman abinda yasa a gaba kuma a wannan karon shine karbe mulki a shekarar 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel