Nigerian news All categories All tags
PDP ce ta dauki nauyin kashe-kashen Filato don batawa Buhari suna - BMO

PDP ce ta dauki nauyin kashe-kashen Filato don batawa Buhari suna - BMO

Kungiyar sadarwa ta shugaba Muhammadu Buhari (BMO) ta bayyana cewa masu adawa da jam'iyyar APC ne suka kitsa kashe-kashen jihar Filato kawai don su bata wa Buhari suna.

Kamfanin dillanci labarai na kasa (NAN) ta ruwaito cewa ciyaman din kungiyar, Austin Braimo da sakataren sa Cassidy Madueke na suka bayar da wannan sanarwan a ranar Juma'a a Abuja.

Sanarwan ta ce masu adawa da jam'iyyar APC ne kon son jefa jam'iyyar cikin tsaka mai wuya sakamakon yadda ta gudanar da gangamin taron ta cikin nasarar.

KU KARANTA: Yaki da rashawa: Kotu ta tisa keyar tsohon shugaban PDP zuwa gidan yari

An dai ce jam'iyyar PDP ce ta dauki nauyin kisar gillar saboda ta shafa wa shugaba Buhari kashin kaza tare da dakile nasarorin da jam'iyyar APC ta samu a yanzu.

PDP ce tayi sanadin kashe-kashen Filato don batawa Buhari suna - BMO

PDP ce tayi sanadin kashe-kashen Filato don batawa Buhari suna - BMO

Sanarwan ta bayyana cewa an aikata wannan abin bakin cikin ne a lokacin da deleget din jam'iyyar APC ke komawa gidajensu a arewacin Najeriya ta jihar Filato inda aka tsare su kuma akayi musu kisar gilla.

"An gano cewa wanda suka aikata kashe-kashen sun saka shinge a titi inda suka rika tare mutane suna kashe su babu gyara babu dalili.

"Misalin mutane 90 ne aka kashe a kusa da Jos, babban birnin jihar Filato.

"BMO tana kira ga 'yan Najeriya su cigaba da bawa shugaba Buhari goyon baya tare da yin watsi da marasa kishin kasa da ke kokarin shafa wa shugaban kasa da jam'iyyar sa kashin kaza."

Kungiyar kuma ta mika sakon ta'aziyya ga iyalan wanda suka rasa yan uwansu tare da yin addu'a Allah ya gafarta musu ya kuma bawa wanda suka sami raunuka lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel