Nigerian news All categories All tags
DSS sunyi babban kamu a jihar Anambra

DSS sunyi babban kamu a jihar Anambra

Hukumar 'yan sandan farin kaya ta Najeriya (DSS) ta kama wasu mutane biyar a jihar Anambra, wadanda suke da hannu a wurin karbar kudi a kasuwa ta hanyar da bata dace ba

DSS sunyi babban kamu a jihar Anambra

DSS sunyi babban kamu a jihar Anambra

Hukumar 'yan sandan farin kaya ta Najeriya (DSS) ta kama wasu mutane biyar a jihar Anambra, wadanda suke da hannu a wurin karbar kudi a kasuwa ta hanyar da bata dace ba. Kwamishinan kasuwanci na jihar Dr. Christian Madubuko, yace masu laifin sun hada shugabannin kasuwar wadanda suke juyar da kudin gwamnati zuwa aljihunan su, ta hanyar bada raciti na karya, wanda ba na gwamnati bane.

DUBA WANNAN: An harbi wani yaron dan takarar gwamna

Madubuko wanda ya samu rakiyar hukumar DSS, ya shawarci jama'a dasu kai rahoton duk wanda suka kama da irin wannan halayyar, inda ya bayyana cewar gwamnatin jihar tana bukatar kudi domin kawo cigaba.

Shugaban kasuwar Ogbaru, Cif Victor Nwawuzie, ya musanta zargin da ake yi musu, inda yace shi iya kudin da yasan an ce ya karba shine kudin wurin ajiye kaya, wanda kuma racitin shi ya fito daga wurin gwamnati ne.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel