Ana shirin takawa masu amfani da shafukan sadarwa na zamani burki

Ana shirin takawa masu amfani da shafukan sadarwa na zamani burki

Majalisar Tarayyar Najeriya ta bayyana cewa masu amfani da Facebook da Twitter da irin su Instagram da dai sauran shafukan sada zumunta na zamani za su gamu da wasu sauye-sauye daga Gwamnati.

Shugaban kwamitin na’urori na zamani a Majalisa watau ICT Sanata AbdulFatai Buhari ya bayyana cewa ‘Yan Najeriya na cin zarafin kafofin na zamani su na yin abin da ya wuce gona da iri don haka dole a taka masu burki.

Ana shirin takawa masu amfani da shafukan sadarwa na zamani burki

Majalisar Dattawa za ta takawa masu hawa shafukan sadarwa lamba

Sanata Buhari ya bayyana wannan ne wajen wani taro da aka yi kan mau barna a shafukan gizo a babban Birnin Tarayya Abuja. ‘DanMajalisar Dattawan yace idan aka rabu da ‘Yan Najeriya su na iya jefa kasar cikin wani rikici.

KU KARANTA: Takaitaccen Tarihin Hassan Sarkin Dogarai na Kano

Sanatan ya bayyana cewa wasu a Kasar na yada labaran da ba dai-dai bane saboda kokarin ganin bayan ‘Yan adawar su na siyasa. Don haka ne dai aka kawo kudirin da zai kawo gyara a gaban Majalisan kasar kuma har batun yayi nisa.

Daily Trust ta rahoto cewa Ministan sadarwa na Kasar Adebayor Shittu dai yace Ma’aikatar sa za su hada kai da Ofishin mai bada shawara kan harkokin tsaro da kuma Majalisa domin maganin masu yada labarai na bogi a kafofin sadarwan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel