Nigerian news All categories All tags
2019: Ana sa ran matasa da yawa za su yi takara - Saraki

2019: Ana sa ran matasa da yawa za su yi takara - Saraki

Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya bayyana cewa ana sanya ran matasa da yawa za su fito takara a zaben 2019 sakamakon sanya hannu da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a dokar ba matasa damar shiga siyasa.

Ya yi Magana ne a ranar Juma’a a Abuja wajen bikin murnar amincewa da dokar ba matasa damar yin siyasa.

Saraki wanda ya samu wakilcin hadiminsa, Kinsley Amaku ya bayyana matasan Najeriya a matsayin masu son cigaban dimokradiyya.

2019: Ana sa ran matasa da yawa za su yi takara - Saraki

2019: Ana sa ran matasa da yawa za su yi takara - Saraki

Shugaban majalisar dattawan ya yi murnar wannan cigaban inda ya bayyana cewa hakan zai ba matasa da dama shiga harkar siyasa a zaben 2019.

KU KARANTA KUMA: Har yanzu Kwankwaso na jam’iyyar APC – Jigon jam’iyyar

A baya Legit.ng ta rahoto cewa dan takarar shugabancin kasa karkashin lemar Peoples Democratic Party (PDP), Dr Datti Baba-Ahmed, ya fada ma jam’iyyar cewa su bashi tikitin takarar shugabancin kasa, cewa zai kora shugaban kasa Muhammadu Buhari gida a zaben shekara mai zuwa.

Ya bayyana hakan ne sakatariyar jam’iyar ta kasa dake Abuja lokacin da ya je kaddamar da kudirinsa na tsayawa takara a ranar Juma’a.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku bide mu a shafukanmu na kafofin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel