Nigerian news All categories All tags
Tambuwal ya yi magana a kan alakanta shi da kashe-kashen jihar Filato

Tambuwal ya yi magana a kan alakanta shi da kashe-kashen jihar Filato

Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya yi kira ga 'yan Najeriya suyi watsi da wani faifan bidiyo da ake yadawa inda ake ikirarin cewa yana da hannu cikin kisar gillar da akayi wa sama da mutane 200 a wasu kauyuka a karamar hukumar Barkin Ladi na Jihar Filato.

A yayin da ya tafiya yin jaje ga gwamnati da mutane Filato, Tambuwal ya ce "bani da hannu cikin wannan lamarin, bai dace wani ya nemi alakanta ni dashi ba, ya kamata mutane suyi watsi da wannan bidyon da ke kokarin kawo rashin jituwa tsakanin al'umma."

Tambuwal ya yi magana a kan alakanta shi da kashe-kashen jihar Filato

Tambuwal ya yi magana a kan alakanta shi da kashe-kashen jihar Filato

KU KARANTA: Yaki da rashawa: Kotu ta tisa keyar tsohon shugaban PDP zuwa gidan yari

Tambuwal ya kai ziyarar ne tare da gwamnonin jihohin Bauchi da Zamfara da Benue da Imo da Delta da Nasarawa tare kuma da mataimakan gwamnonin jihohin Kaduna da Akwa Ibom da Oyo da Ondo da kuma Edo.

Gwamna Tambuwal ya ce jihar Filato kamar gida ne a wajensa shi yasa ya ke yawan ziyartar jihar tun lokacin da ya zama gwamna.

Ya kuma ce ya janyo hankalin hukumomin tsaro game da bidiyon inda suka bayyana masa cewa an kirkire shi tun lokacin mulkin da baya da shude.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel