Nigerian news All categories All tags
Shari'a sabanin hankali: sun saci abin dubu 20 an caje su dubu 300

Shari'a sabanin hankali: sun saci abin dubu 20 an caje su dubu 300

A ranar juma'ar nan ne aka gurfanar da wasu mutane uku, da aka kama da laifin satar waya wadda kudin ta ya kai naira dubu ashirin, a gaban babbar kotun Majistire dake Badagry a jihar Lagos

Shari'a sabanin hankali: sun saci abin dubu 20 an caje su dubu 300

Shari'a sabanin hankali: sun saci abin dubu 20 an caje su dubu 300

A ranar juma'ar nan ne aka gurfanar da wasu mutane uku, da aka kama da laifin satar waya wadda kudin ta ya kai naira dubu ashirin, a gaban babbar kotun Majistire dake Badagry a jihar Lagos. Mutanen da aka bayyana sunayen su da Obinna Okafor, mai shekaru 24, da kuma Sesay Kappo mai shekaru 20, wanda duka basu bayyana adireshin su ba, ana zargin su da laifin sata.

DUBA WANNAN: Yanzu - yanzu: Hukumar EFCC tayi babban kamu

A bayanin da mai karar yayi Insp. Akpan Ikem yace, an kama masu laifin a ranar 19 ga watan Yulin nan a gida mai lamba 1, dake kan layin Hundeyin St., Idale, Badagry.

Uko ya bayyana cewar wadanda ake zargin sun saci wayar ne a gidan wani mutum mai suna Mista Ovi Tanumi.

An bayyana laifin su a matsayin wanda ya sabawa sashe na 278 na dokar jihar Lagos, a shekarar 2011.

Majiyar mu Legit.ng ta samu rahoton cewar an yankewa masu laifin hukuncin shekaru uku a gidan kaso. Sannan alkalin kotun Jimoh Adefioye ya bukaci masu laifin da su bada naira 100,000 kowanne a matsayin kudin beli, sannan kuma su gabatar da shaidu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel