Wauta da jahilci ya saka mutane mutuwa yayin gobarar tankan dakon man fetur na jiya

Wauta da jahilci ya saka mutane mutuwa yayin gobarar tankan dakon man fetur na jiya

Bayan afkuwar gobarar tankan dakon man fetur a gadan Otedola da ya yi sanadiyar rasuwar mutane da dama tare da asarar dukiyoyi, wani wanda abin ya faru a idanunsa ya ce wauta da jahilci ne ya janyo rasuwar mutanen a jiya.

A cewar ganau din da ya yi ikirarin cewa wayar salularsa ta bata a sakamakon gobarar, ba laifin direban tankar bane, laifin direban karamar motar ne da ya sauka fasinja a wurin da ba'a tsayawa kuma ya kutsa kan titi ba tare da ya duba madubin motarsa ba ko da mai zuwa a bayansa.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun tabbatar da kisar gillar da akayi wa makiyaya 6 tare shanunsu 150 a jihar Nasarawa

Ga dai wani sashi daga cikin sakon da ya rubuta a shafinsa na twitter @Otunbakush

"Waya ta bata sakamakon hatsarin tankar da ta faru a jiya. Da farko dai ba laifin direban karamar motar ne da ya sauka fasinja a wurin da ba'a tsayawa kuma ya kutsa kan titi ba tare da ya duba madubin motarsa ba ko da mai zuwa a bayansa.

"Direban tankar ya yi kokarin kare afkuwar hatsarin hakan yasa ya taka birkinsa ya bugi ginin da ke raba titi kuma motar ta kife amma bata kama da wuta ba, sai dai a maimakon mutane suyi nesa daga wajen don ceto rayuwarsa, sai suka fara kokarin ceton motocinsu.

"Akwai wani mutum mai Camry wanda ya bata lokaci yana kokarin reverse a maimakon ya fice ya tsira da rayuwarsa domin. Abinda ya da ce suyi shine su tsira da ransa daga baya sai ayi batun motocin amma saboda wauta basuyi hakan ba.

"Wasu mu sun zauna cikin motocinsu ne suna daukan bidiyo ne a maimakon su gudu, jim kadan wuta tayi musu kawanya kuma suka rikice, a lokacin ne suka fara kokarin ficewa amma sunyi latti, Allah ya jikansu amma wauta da jahilci ne ya kashe mutane a gadar nan."

Wauta da jahilci ya saka mutane mutuwa yayin gobarar tankan dakon man fetur na jiya

Wauta da jahilci ya saka mutane mutuwa yayin gobarar tankan dakon man fetur na jiya

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel