Nigerian news All categories All tags
Guguwar iskar Katsina: Gwamnatin tarayya za ta bayar da tallafi ga wadanda abun ya shafa - Buhari

Guguwar iskar Katsina: Gwamnatin tarayya za ta bayar da tallafi ga wadanda abun ya shafa - Buhari

A ranar Juma’a, 29 ga watan Yuni, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin cewaa gwamnatin tarayya za ta tallafawa wadanda annobar guguwar iska ya ritsa das u a jihar Katsina.

Shugaban kasar yayi alkawarin ne bayan Gwamna Aminu Bello Masari ya lissafa asarar da jihar tayi sakamakon lamarin a matsayin naira biliyan 2.3.

Ya c e ya kasance a jihar domin yiwa wadanda abun ya shafa jaje saboda rashin da aka lissafa ya zarce tunani.

Guguwar iskar Katsina: Gwamnatin tarayya za ta bayar da tallafi ga wadanda abun ya shafa - Buhari

Guguwar iskar Katsina: Gwamnatin tarayya za ta bayar da tallafi ga wadanda abun ya shafa - Buhari

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Buhari yayi alkawarin cewa zai goyi bayan duk wani yunkuri da zai kawo inganci ga lamarin tsaro a nahira Afrika ta Kudu.

KU KARANTA KUMA: Kashe-kashe: Gwamnoni sun kai ziyarar jaje jihar Plateau

A cewar wata sanarwa daga hadiminsa, Femi Adesina, shugaban kasar yayi Magana ne yayinda ya amshi bakuncin shugaban kungiyar kasashen Afrika kuma shugaban kasar Togo, Faure Gnassingbe, a Katsina.

Buhari yace a yanzu yan ta’adda na addaban iyakokin kasashe, sannan kuma cewa babu kasar da zata iya wannan yaki ita kadai.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku bide mu a shafukanmu na kafofin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel