Nigerian news All categories All tags
Kashe-kashe: Gwamnoni sun kai ziyarar jaje jihar Plateau

Kashe-kashe: Gwamnoni sun kai ziyarar jaje jihar Plateau

Kungiyar gwamnonin Najeriya sun ziyarci jihar Plateau domin yiwa mutane da gwamnatin jihar jaje akan kisan mutanensu da ake zargin makiyaya suka yi.

Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Zamfara, Abdul’Azeez Yari ne ya jagoranci takwarorin nasa a ziyarar jajen da suka kai a ranar Juma’a.

Sun samu tarba daga Gwamna Simon Lalong da sauran manyan jami’an gwamnati a gidan gwamnatin dake garin Jos, babban birnin jihar.

Kashe-kashe: Gwamnoni sun kai ziyarar jaje jihar Plateau

Kashe-kashe: Gwamnoni sun kai ziyarar jaje jihar Plateau

Da yake Magana a madadin kungiyar, Yari ya sanar da Lalong cewa mambobin kungiyar sun yi ziyarar ne domin suna ganin akwai bukatar a tausayawa wadanda abun ya shafa da mutanen jihar sannan kuma su bada gudunmawarsu wajen yaki da ta’addanci a fadin kasar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Tirela ya yi karo da tankar mai a hanyar Suleja-Minna

Ya yi Allah wadai da kashe-kashen da kuma sanar da gwamnan Plateau game da shirin kungiyar na tattaunawa da shugabannin tsaro don kawo mafita mai kullewa kan matsalolin tsaro a Najeriya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku bide mu a shafukanmu na kafofin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel