Nigerian news All categories All tags
Kotu ta wanke tsohon shugaban hukumar Sojin sama tatas daga laifin Zamba

Kotu ta wanke tsohon shugaban hukumar Sojin sama tatas daga laifin Zamba

Kamar yadda shafin jaridar Premium Times ya bayyana, babbar kotun tarayya dake babban birnin kasar nan na Abuja ta sallami tsohon shugaban hukumar sojin sama Najeriya, Alkali Mamu.

A watan Yunin shekarar 2016 da ta gabata ne aka zargi tsohon shugaban hukumar da laifin karbar tukwici yayin da yake bakin aiki.

Kamar yadda hukumar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa watau EFCC ta bayyana, Mista Mamu ya karbi tukwicin na $300, 000 da kuma N5.9m dangane da sayen wasu motoci na alfarma daga hannun wani mamba na kwamitin tsare-tsaren Ma'aikatar tsaro ta kasa.

Kotu ta wanke tsohon shugaban hukumar Sojin sama tatas daga laifin Zamba

Kotu ta wanke tsohon shugaban hukumar Sojin sama tatas daga laifin Zamba

Hukumar ta kuma zargi tsohon shugaban hukumar sojin da karbar wasu Motoci biyu na alfarma da darajar su ta kai kimanin Naira Miliyan 27 daga hannun kamfanin Societe D’ Equipment Internationaux Nigeria Ltd, dake da yarjejeniyar kwangila da hukumar sojin sama ta Najeriya.

KARANTA KUMA: Kasafin 2018: Tsageru sun yiwa 'Yan Majalisun Neja Delta kashedi

A yayin zartar da wannan hukunci a ranar Juma'a ta yau, Alkali Garba Salisu ya bayyana cewa masu gabatar da karar Mista Mamu sun gaza gabatar da jawabai na shaida da hujjoji kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar.

Bugu da kari Alkalin ya bayyana cewa, hukumar ta gaza bayar da cikakkiyar hujja da za su tabbatar da zargin da take yiwa tsohon shugaban hukumar sojin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel