Nigerian news All categories All tags
Yaki da rashawa: Kotu ta tisa keyar tsohon shugaban PDP zuwa gidan yari

Yaki da rashawa: Kotu ta tisa keyar tsohon shugaban PDP zuwa gidan yari

Babban kotun jihar Legas ta bayar da umurnin tsare ciyaman din jam'iyyar PDP na jihar Ondo, Clement Faboyede da kuma direktan yakin neman babban zaben 2015 a jihar Modupe Adetokunbo a gidan yari.

Alkalin kotun, Justice Saliu Saidu ya bayar da umurnin tsare shugabanin biyu ne bayan an gurfanar da su kan zargin karkatar da N500 miliyan gabanin babban zaben kasa na shekarar 2015.

Yaki da rashawa: Kotu ta tisa keyar tsohon shugaban PDP zuwa gidan yari

Yaki da rashawa: Kotu ta tisa keyar tsohon shugaban PDP zuwa gidan yari

Ana tuhumar mutanen biyu da aikata laifuka uku wanda suka hada da makirci da karkatar kudaden al'umma kamar yadda lauyoyin hukumar yaki da masu yiwa arzikin kasa zagon kasa EFCC.

KU KARANTA: Wauta da jahilci ya saka mutane mutuwa yayin gobarar tankan dakon man fetur na jiya

Lauyan EFCC, Mr Ekene Iheanacho ya shaidawa kotu cewa Faboyede da Adetokunbo da sauran sun aikata laifin ne a ranar 27 ga watan Maris na shekarar 2015.

Iheanacho ya yi ikirarin cewa sun hada baki suka karbi kudi N500 miliyan daga hannun wani Owolanke Micheal ba tare da amfani da banki ba wanda hakan ya sabawa doka.

A cewar lauya mai shigar da kara, laifukan da suka aikata ya ci karo da sashi 1 na dokar satar kudi na shekarar 2011 kuma akwai hukuncin da sashi na 16(2) ya tanada.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel