Nigerian news All categories All tags
Kuma dai: An sake hatsarin mota a Legas, an rasa rayyuka biyu

Kuma dai: An sake hatsarin mota a Legas, an rasa rayyuka biyu

- An sake samun wani hatsarin mota a Legas da ya yi sanadiyar rasuwar mutane biyu

- Wannan na zuwa ne kwana daya bayan konewar tanka dauke da man fetur da ya yi sanadiyar rasuwar mutane da dama a Legas din

- Wanda abin ya faru a idanunsu sun ce wani mai motar kabu-kabu ne ya buga ma wata Hummer bus

Bayan afkuwar hatsarin mota da ya janyo konewar tanka dauke da man fetur da ya yi sanadiyyar rasuwar mutane tara tare da kone motoci 54 a ranar Laraba a gadan Otedola da ke Legas, an kuma sake samun wata hatsarin motar da ya yi sanadiyar rasuwar mutane biyu.

Hatsarin ya afku ne a ranar Alhamis a yayin da wani mai tukin motar kabu-kabu wanda akafi sani da Danfo ya fadawa wata Hummer bus a kokarinsa na kaucewa jami'an kiyaya hadura na Legas.

Kuma dai: An sake hatsarin mota a Legas, an rasa rayyuka biyu

Kuma dai: An sake hatsarin mota a Legas, an rasa rayyuka biyu

KU KARANTA: 'Yan sanda sun tabbatar da kisar gillar da akayi wa makiyaya 6 tare shanunsu 150 a jihar Nasarawa

Rotimi Adebeshin, wanda hatsarin ya faru a idanunsa ya ce mai motar hayan yana kokarin kutsawa ta barauniyar hanya ne saboda cinkoson da ya faru sakamakon konewar da tankar ta yi a ranar Laraba.

A kalla mutane tare na suka riga mu gidan gaskiya a ranar Laraba sakamakon gabarar da tankar man fetur din ta yi kuma motocci 54 ne suka kone kurmus.

Mutane masu wucewa da kuma jami'an kare haddura har wasu masu ababen hawa sun garzaya don taimakawa wadanda hatsarin ya ritsa da su kuma suka garazaya da su asibitoci don ayi musu magani.

Jaridar Premium Times ta gano cewa a kalla mutane 20 ne suka sami rauni sakamakon hatsarin motar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel