Nigerian news All categories All tags
Shugaba Buhari ya rattaba hannu kan wasu sabbin Dokoki 2 a Najeriya

Shugaba Buhari ya rattaba hannu kan wasu sabbin Dokoki 2 a Najeriya

A ranar Alhamis din da ta gabata ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya rattaba hannu kan wasu sabbin dokoki biyu a kasar nan kamar yadda mai sadarwa sa kan harkokin majalisar dattawa ya bayyana, Mista Ita Enang.

Mista Enang ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai na fadar shugaban kasa da ya bayyana cewa, sabbin dokokin sun hadar da ta Horar da manyan Likitoci da kuma cibiyar gudanar da harkokin wutar lantarki.

A cewar Mista Enang, sabuwar dokar ta kiwon lafiya za ta bayar da damar kaddamar da shirin horas da malaman asibiti da suka yi karatun digiri a fannin nazari daban-daban, inda Makarantar ci gaba da karatun kiwon lafiya ta Najeriya za ta dauki nauyin gudanar da shirin.

Shugaba Buhari ya rattaba hannu kan wasu sabbin Dokoki 2 a Najeriya

Shugaba Buhari ya rattaba hannu kan wasu sabbin Dokoki 2 a Najeriya

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan sabuwar doka za ta bayar da dama ta inganta wa nagarta da gogayyar malaman asibiti ta hanyar shirin da ta tanadar.

DUBA WANNAN: 'Yan Bindiga sun kashe wani manemin takarar gwamna a jihar Akwa Ibom

Hakazalika dokar zata karfafa gwiwar al'ummar wasu kasashen wajen neman lafiya a kasar nan ta Najeriya tare da bunkasa amincin harkokin lafiya na kasar nan.

Dangane da dokar harkokin wutar lantarki, hadimin na shugaba Buhari ya bayyana cewa za ta saukaka adadin kudin wuta daga kaso 30 zuwa 10 cikin 100.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel