Nigerian news All categories All tags
Matar basarake wacce aka sace ta bayyana irin halin da ta riski kanta a hannun masu garkuwa

Matar basarake wacce aka sace ta bayyana irin halin da ta riski kanta a hannun masu garkuwa

Uwargidan wani Basarake a jihar Ondo Alauga na Auga dake karamar hukumar Akoko north east dake jihar, Olukemi Agunloye wacce masu garkuwa da mutane suka saki tace an tursasa ta shan ruwan da aka ajiye domin shan dabbobi.

An sace Uwargidan basaraken da direbansu a tsakanin Auga da Ise Akoko a hanyarsu na zuwa Ugbe-Akoko dake yanki guda.

Kakakin yan sandan jihar, Femi Joseph ne ya tabbatarwa da gidan talbijin din Channels batun sakin na su.

Da farko dai masu garkuwan sun bukaci a basu fansar naira miliyan 20 amma babu cikakken bayani kan ko an biyasu abunda suka bukata.

KU KARANTA KUMA: Sarki ya karrama yaron da ya haddace cikakken Al-Qur'ani a shekara 3

Wata majiya tace a yanzu haka matar sarkin da direban na kwance a asibiti domin samun kulawar likita.

A cewar ahlin gidan, masu garkuwan sun lallasa gimbiyar sosai sannan sun yi mata horo da yunwa na tsawon kwanaki uku sannan suka bata ruwan dabbobi ta sha.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku bide mu a shafukanmu na kafofin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel