Nigerian news All categories All tags
2019: Sule Lamido ya jaddada cewar Buhari ya gaza ba zai iya mulkin ba, a wata ziyara da ya kaiwa Wadata

2019: Sule Lamido ya jaddada cewar Buhari ya gaza ba zai iya mulkin ba, a wata ziyara da ya kaiwa Wadata

- Bayan samun nasara a kotu Sule Lamido ya kaiwa uwar jam'iyyar PDP ziyara da rokon iri

- A yayin jawabinsa lokacin ziyarar ne tsohon gwamnan yayi jirwaye mai kama da wanka ga shugaban kasa Muhammadu Buhari

Bayan Kwanaki 2 da ziyarar da tsohon mataimakin shugaban kasa kuma mai neman Jamiyyar PDP ta tsayar da shi takarar shugabancin kasar nan wato Alh. Atiku Abubakar.

Sai ga shi tsohon gwamnan Jihar Jigawa wanda shi ma ya ke zawarcin kujerar shugabancin kasar a dai tutar Jamiyyar ta PDP ya kaiwa masu ruwa da tsaki akan shugabancin Jamiyyar, inda ya bayyana musu sha'awarsa ta neman tsayawa takarar shugabancin kasar nan a tutar Jamiyyar a zaben 2019.

2019: Sule Lamido ya jaddada cewar Buhari ya gaza ba zai iya mulkin ba, a wata ziyara da ya kaiwa Wadata

2019: Sule Lamido ya jaddada cewar Buhari ya gaza ba zai iya mulkin ba, a wata ziyara da ya kaiwa Wadata

Sule Lamido wanda ya bayyana tare da rakiyar Tsohuwar ministar harkokin kasashen waje, Josephine Anenih da wasu manyan ‘yan Jamiyyar PDP da wasu masu take masa baya.

A jawabinsa yayin ziyarar Sule Lamido ya bayyanawa shugabancin Jamiyyar cewa shi jigo ne a siyasar kasar nan wanda zai iya kai kasar nan tudun Mun tsira, matukar ya kai ga nasarar zama shugaban kasa.

Sannan kuma ya bukaci shugabancin Jamiyyar da ya yi duk mai yiwuwa wajen hada kai don ganin sun kai dukkanin wani dantakarar jamiyyar APC zata tsayar kasa a zaben 2019 da ya ke tafe.

Da yake bayyana irin salon gwamanatin shugaban kasa Muhammadu Buhari kuwa, kira yayi ga ‘yan kasar nan da su sani cewa dama tun asali shugaban kasa Buhari yana da tarihi yin mulki cikin rikice rikice, wanda wannan ne ya sa yanzu ma rikici ke cigaba da faruwa a sassan kasar nan.

KU KARANTA: Kotu ta wanke tsohon Gwamnan Jigawa Alhaji Sule Lamido

Sannan ya shaida cewar babban Burinsa shi ne dawowa da kasar nan martabarta domin ‘yan kasar nan su amfana da arzikin da Allah yayi mata.

Kana yayi kira ga dukkan wani mai fatan ganin hakan da ya taho su hada karfi waje guda domin kaiwa ga gaci.

A nasa bangaren kuwa shugaban Jamiyyar PDP na kasa Prince Uche Secondus, bayyana Sule Lamidon yayi a matsayin jajirtaccen dan kishin kasa wanda ya dauki halin 'yan mazan jiya irinsu Sir Ahmadu Bello, Chief Obafemi Awolowo da Dr. Nnamdi Azikiwe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel