Nigerian news All categories All tags
Ka hukunta masu a hannu a kashe - kashen jihar Filato - Sakon Gwamnoni ga Shugaba Buhari

Ka hukunta masu a hannu a kashe - kashen jihar Filato - Sakon Gwamnoni ga Shugaba Buhari

Gwamnonin jihohin Najeriya 36 sun bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi gaggawar fito da wadanda suke da hannu a kashe - kashen da ake yi jihar Filato kuma ya dauki kwakkwaran mataki akan su wurin gabatar hukunci akan su

Ka hukunta masu a hannu a kashe - kashen jihar Filato - Sakon Gwamnoni ga Shugaba Buhari

Ka hukunta masu a hannu a kashe - kashen jihar Filato - Sakon Gwamnoni ga Shugaba Buhari

Gwamnonin jihohin Najeriya 36 sun bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi gaggawar fito da wadanda suke da hannu a kashe - kashen da ake yi jihar Filato kuma ya dauki kwakkwaran mataki akan su wurin gabatar hukunci akan su.

Majiyar mu Legit.ng ta kawo rahoton irin tashin hankalin da al'ummar jihar suka shiga sanadiyyar kisan gillan da aka yiwa sama da mutane 100 a jihar.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa kabilar Himba basa yin wanka

A zaman da gwamnonin jihohin Najeriya suka yi a Abuja jiya, gwamnonin sun bukaci yin taro da manyan manyan kasar nan domin kawo karshen kashe - kashen da ake yi a jihar.

Shugaban kungiyar gwamnonin na Najeriya, Abdulaziz Yari, wanda yayi magana da manema labarai jim kadan bayan sun tashi daga taron, gwamnan yace sun tattauna akan abubuwa da dama da suke addabar kasar nan musamman ma kashe - kashen da ake yi a jihar Filato.

Bayan haka kuma gwamnonin sun nuna godiyar su ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da Mataimakin sa Yemi Osinbajo da irin kokarin da suke nunawa domin ganin an kawo karshen rikicin a jihar. Sannan sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi iya bakin kokarin sa wurin hukunta duk wanda aka kama da laifi a kashe - kashen da yake faruwa a jihar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel