Dakarun sojin Operation Lafiya Dole sun kau da yan ta’addan Boko Haram a kauyen Gawasa
Dakarun sojin Operation Lafiya Dole sun kau da yan ta’addan Boko Haram a kauyen Gawasa dake karamar hukumar Guzamala dake jihar Borno.
Sun yi arangama da yan ta’addan ne a wani aikin kakkaba da suke gudanarwa a yankin.
An kawar da yan ta’adda guda hudu a harin, sannan kuma sun samo wasu kayyayaki da suka hada da Babura 5, injinan babur 3, tayoyi 2, spirit lita 250, buhuhunan pilawa 2, buhun shinkafa daya, biredi guda 100.
Lita 5 na man gyada guda 60, sabulun wanki kwalaye 4, kutsoshi, cajan waya da sauransu.
Ga hotunan a kasa:
KU KARANTA KUMA: Sule Lamido ya kayar da gwamnatin jihar Jigawa a kotu
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku bide mu a shafukanmu na kafofin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng