Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira Katsina yanzu, daga nan zai tafi Mauritania gobe

Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira Katsina yanzu, daga nan zai tafi Mauritania gobe

Shugaban Muhammadu Buhari ya isa jiharsa, jihar Katsina a yau Juma’a, 29 ga watan Yuni 2018 domin ziyara ta musamman.

Legit.ng na bada rahoton cewa jirgin shugaba Buhari dauke da shi da wasu mukarrabansa ya dira babban filin jirgin saman Umaru Musa Yar’Adua International Airport Katsina misalin karfe 9:56 na safiyar nan.

Shugaban kasan ya samu tarba ne daga gwamnan jihar, Mal Aminu Bello Masari, da wasu manyan jami’an gwamnatin jihar.

Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira Katsina yanzu, daga nan zai tafi Mauritania gobe

Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira Katsina yanzu, daga nan zai tafi Mauritania gobe

A nan jihar Katsinan, shugaba Buhari zai karbi bakuncin shugaban kasar Togo, Faure Gnassingbe Eyadema.

KU KARANTA: Jerin jihohi da yawan mutanen da aka kashe daga watan Junairu zuwa yau, game da binciken Amnesty

Kana zai kai ziyarar ban girma ga sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumuni Usman, inda zai tattauna da malaman da masu unguwa kan da masu ruwa da tsaki a jihar kan abubuwan da suka shafi cigaban kasa.

Buhari zai yi amfani da wannan dama wajen jajentawa gwamnatin jihar da jama’arta kan annobar mabaliyar da ya afka musu inda mutane 6 suka hallaka kuma akayi hasaran gidaje 530.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel