Nigerian news All categories All tags
Kasafin 2018: Tsageru sun yiwa 'Yan Majalisun Neja Delta kashedi

Kasafin 2018: Tsageru sun yiwa 'Yan Majalisun Neja Delta kashedi

A ranar Alhamis din da ta gabata ne tsagerun Neja Delta suka kaddamar da 'yan Majalisar Dokoki ta tarayya dake wakiltar yankin su a matsayin makiyan ci gaba tare da yin barazanar maganin su da tarwatsa duk wasu kadarorin su dake yankin.

Kamar yadda shafin jaridar Vanguard ya ruwaito, tsagerun sun zargi 'yan Majalisar masu wakiltar yankunan su da amincewa wajen cire duk wasu muhimman ayyuka gine-gine na yankin daga cikin kasafin kudin 2018 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattabawa hannu.

Tsagerun yayin ganawar su a gabar Tekun Benin dake Egbema a jihar Delta, sun kushe tanadin da kasafin kudin ya yiwa yankin su baya ga ikirarin su na cewar yankin shine jagaba wajen samar da duk wata dukiya a kasar nan daga albarkatun man fetur na yankin.

Kasafin 2018: Tsageru sun yiwa 'Yan Majalisun Neja Delta kashedi

Kasafin 2018: Tsageru sun yiwa 'Yan Majalisun Neja Delta kashedi

A sanadiyar wannan fusata ne tsagerun suka yi tir da caccakar 'yan majalisun tarayya masu wakiltar yankunan su da cewar "rashin fahimta, shashanci, gami da dakushewar kwakwalwa ce ta sanya 'yan majalisar suka gaza fahimtar nauyin da rataya a wuyansu."

"Kungiyar tsagerun ta RNDA ta kaddamar ta 'yan majalisar tarayya masu wakiltar yankin Neja Delta a matsayin makiya na gaske ga ci gaban yankin su kuma sai ta mummunan hukunci a kansu ta hayar tarwatsa duk wasu kadarori da suka mallaka a yankin."

DUBA WANNAN: Gwamnonin Najeriya za su gana da Shugabannin tsaro na Kasa

Kungiyar take cewa, "babu abinda 'yan majalisar ke yi domin ci gaban yankin su sai dai naɗe hannayen su tare da rage kaso na muhimman ayyuka daga cikin kasafin kudi da za su kawo ci gaba a yankin su kuma su kyale na sauran yankunan kasar."

"Abin kunya ne da kuma lalacewa a bangaren 'yan majalisar mu dake majalisar dokoki ta tarayya su sanya idanu tare da amincewa da rashin adalcin da ake yiwa yankin baya ga cewar shugaban kasa ya riga da ware wani kaso na kudade domin gudanar da muhimman ayyuka da za su inganta rayuwar al'ummar mu."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel