Nigerian news All categories All tags
Shugaba Buhari zai tafi kasar Mauritania gobe

Shugaba Buhari zai tafi kasar Mauritania gobe

Shugaba Muhammadu Buhari a gobe Asabar, 30 ga watan Yuni, 2018 zai garzaya birnin Nouakchott, kasar Mauritania domin halartan taron gamayyar kasashen Afrika na 31 da za’ayi ranan 1 da 2 ga watan Yuli, 2018.

Wannan labara na shigowa ne bayan shugaban kasa ya rattaba hannu kan sabon dokan horar da likitocin gida.

Jaridar Thisday ta samu rahoton cewa shugaban kasan zai tafi garin Daura, jihar Katsina a yau Juma’a, sannan ya tafi Nouakchott gobe domin haduwa da sauran shugabannin kasasehn duniya a taron da a fara ranan 25 ga wata.

KU KARANTA: Zamu dawwama a talauci muddin bamu rage haihuwa barkatai ba - Ministan Buhari

Taron na wannan shekaran dai na ke take : “Samun nasara kan yaki da rashawa: Yadda za’a kawo sauyi nahiyar Afrika”. Shugaba Muhammadu Buhari ne zai gabatar da jawabi na musamman akan wannan take.

Sannan shugaban gamayyar kasashen Afrikan kuma shugaban kasan Ruwanda, Paul Kagama, zai gabatar da jawabi kan sauye-sauyen gamayyar, shi kuma shugaban kasan Nijar, Mahamadou Issoufou, zai gabatar da nasa kan kasuwanci a Afirka.

Wannan shi ne karo na farko da za’a yi taron a kasar Mauritania tun bayan kafa ta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel