Nigerian news All categories All tags
'Yan Bindiga sun kashe wani manemin takarar gwamna a jihar Akwa Ibom

'Yan Bindiga sun kashe wani manemin takarar gwamna a jihar Akwa Ibom

A halin yanzu dai tuni jami'an tsaro na hukumar 'yan sanda, sun fara gudanar da bincike kan wani manemin takarar kujerar gwamnatin jihar Akwa Ibom, Okon Iyanam, da 'yan bindiga suka kashe cikin wani Otel dake jihar Ogun.

Shafin jaridar The Punch ya ruwaito cewa, a ranar Larabar da ta gabata ne aka kashe wannan mutum mai shekaru 52 a duniya cikin Otel din Heritage Hotel and Resorts Mowe dake yankin karamar hukumar Obafemi Owode a jihar ta Ogun.

Lamarin ya afku yayin da wasu mutane hudu rike da bindiga suka katse bikin murnar zagoyawar ranar haihuwar Marigayi Orom da ake gudanarwa cikin Otel tare da 'yan uwa da abokan arziki.

Rahotannin sun bayyana cewa, bayan kwace wayoyin salula na dukkanin mahalarta bikin, sun harbi Orom a wuyan sa da harasashi na bindiga inda nan take suka arce abin su.

An yi gaggawar garzaya wa da Marigayi wani asibiti na kurkusa, inda likitoci suka tabbatar da mutuwar sa.

Majiyar rahoton ta bayyana cewa, 'yan bindigar sun kai wannan hari ne da misalin karfe 1.30 na daren ranar Larabar da ta gabata.

DUBA WANNAN: Bankin Duniya zai bayar da bashin $2.1bn domin gudanar da wasu manyan ayyuka 7 a Najeriya

Legit.ng ta fahimci cewa, baya ga kasancewar Marigayi Orom manemin takarar kujerar gwamnatin jihar Akwa Ibom, a yayin rayuwar sa ya kuma kasance babban ma'aikaci a kamfanin sadarwa na Airtel da kuma kamfanin Expertro Energy.

Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da afkuwar wannan lamari na fashi da makami da kuma kisan gilla da ya bayyana cewa tuni bincike ya riga da kan kama.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel