Nigerian news All categories All tags
Sai da na fada wa Kwankwaso kada ya dora Ganduje, gashi yanzu yana dandana kudar sa – Hon Sumaila

Sai da na fada wa Kwankwaso kada ya dora Ganduje, gashi yanzu yana dandana kudar sa – Hon Sumaila

Hon Kawu Sumaila ya yi tsokaci akan rashin jituwar dake tsakanin tsohon gawamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da gwamna mai ci, Abdullahi Umar Ganduje.

A cewar Hon Kawu sai da ya ja wa Kwankwaso kunne kan cewa kada ya kuskura ya daura dan takara ba tare da an bi yadda ka’idar doka ta gindaya ba amma ya ki bi wannan shawara da ya ba shi ya daura Ganduje.

Hakan na dauke ne a tattaunawar da Kawu yayi da jaridar Premium Times.

Hon Sumaila ya kara dacewa duk da wannan matsala da aka samu, shi yana tare da gwamna Abdullahi Ganduje ba Kwankwaso ba saboda Ganduje na tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Sai da na fada wa Kwankwaso kada ya dora Ganduje, gashi yanzu yana dandana kudar sa – Hon Sumaila

Sai da na fada wa Kwankwaso kada ya dora Ganduje, gashi yanzu yana dandana kudar sa – Hon Sumaila

Da aka tambaya shi ko barin Kwankwaso daga APC zai iya kawo wa jam’iyyar tawaya, sai yace tabbas rasa dan siyasa a jam’iyya ya kan kawo wa jam’iyya tawaya tunda ita siyasa da yawanku ne kuke cin zabe, saboda haka kowa so yake ya samu karuwar mutane ba raguwa ba.

A wani lamari na daban, Ministan Kasuwanci da saka jari, Mr. Okechukwu Enelamah ya ce Najeriya za ta cigaba da dawwama cikin talauci muddin yan Najeriya basu dena haihuwan yara barkatai ba.

KU KARANTA KUMA: Shari’ar Maryam Sanda: An samu babban cikas, an sake daga zaman da watanni 3

Ministan ya furta wannan magana ne a ranar Laraba yayin da ya ke tsokaci a kan rahoton Brookings da ta bayyana cewa Najeriya ce kasa mafi yawan al'umma da ke fama da talauci a Najeriya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku bide mu a shafukanmu na kafofin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel