Nigerian news All categories All tags
Yadda wani Matashi ya yi yunkurin halaka kansa da kansa a garin Bauchi

Yadda wani Matashi ya yi yunkurin halaka kansa da kansa a garin Bauchi

Ke duniya ina zaki damu ne? wai wani dalili zai sanya mutum da hankalinsa zai dauki gabaran kashe kansa da kansa, a irin wannan rayuwar da kowa ta kansa yake, kowa na son ya tsira da na bakinsa!

A nan, jaridar Rariya ta ruwaito labarin wani matashi da ya nemi ya hallaka kansa a jihar Bauchi, inda tace wannan matashi ya siyo guba, kuma ya zube shi kaf a cikin abincinsa, Indomie, ba tare da bata lokaci ba ya fara saka loma, tare da yana sane da abinda yake ci.

KU KARANTA: Shugaban gwamnonin APC ya taka rawar Shaku Shaku murnar sakamakon zabe

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a unguwar Railway dake cikin garin Bauchi, inda ta kara da cewa a yayin da wannan dan kasada ke cikin saka loma, sai ya yanke jiki ya fadi, ya fara shure shuren mutuwa.

Yadda wani Matashi ya yi yunkurin halaka kansa da kansa a garin Bauchi

Matashin

Sai dai mutanen da lamarin ya faru a gabansu basu kyale shi ya cika burinsa ba, inda nan take suka laluba aljihunsa, suka samu wata tsohuwar naira dari biyu, anan suka gaggauta sayo masa madara, wanda suka zazzage masa ita a bakinsa.

Amma fa har yanzu babu tabbacin halin da wannan bawan Allah ke ciki, kamar yadda majiyar tamu ta tabbatar, haka zalika babu wani musabbabin yin haka da aka ruwaito.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel