Nigerian news All categories All tags
Shugaban gwamnonin APC ya taka rawar Shaku Shaku murnar sakamakon zabe

Shugaban gwamnonin APC ya taka rawar Shaku Shaku murnar sakamakon zabe

Wani bidiyo na nan yana yawo a shafukan sadarwar zamani na shugaban gwamnonin jam’iyyar APC a yayin da yake tikar rawa son ransa, rawar da ake yayi a Najeriya mai suna ‘Shaku Shaku’, sakamakon siyasarsa ta fara gyaruwa, inji rahoton jaridar The Cables.

Wannan gwamna ba wani bane illa gwamnan jihar Imo, Anayo Rochas Okorocha, wanda jam’iyyar APC reshen jihar Imo ta sullube masa, ma’a ta fita daga ikonsa a sanadiyyar abokan adawarsa na cikin gida ne suka mamaye kujerun shubancin jam’iyyar a jihar.

KU KARANTA: Zargin kashe Mijinta: Shari’ar Maryam Sanda ta samu tasgaro a babbar Kotun Abuja

Sai dai dayake an ce wai ba a nan take ba, an danne bodari ta kai, kuma dama ai tsiyar nasara sai za shi gida, bayan gwamnan ya yi ta fama da bakin cikin abinda ya faru a siyasar jiharsa, sai ga shi ya samu nasarar danne abokan hamayyar tasa a sama.

Bidiyo:

Legit.ng ta ruwaito a wannan karo gwaman ya samu damar kafa irin nasa jama’an a shugabancin jam’iyyar APC ta kasa bayan babban taron jam’iyyar da aka yi a satin daya gabata, inda aka zabe sabbin shuwagabanni.

Bugu da kari gwamnan ya mara ma sabon shugaban jam’iyyar na yanzu, tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshomole baya, kuma ya yi sa’a Oshomolen ya kai labari, don haka ya nuna farin cikinsa da wannan rawa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel