Nigerian news All categories All tags
Akalla mutane 5 sun mutu a sakamakon harbin dan bindiga a wani kamfanin jarida

Akalla mutane 5 sun mutu a sakamakon harbin dan bindiga a wani kamfanin jarida

Akalla mutane biyar ne suka rasa rayukansu bayan da wani dan bindiga ya bude ma wasu yan jarida wuta a yayin da suke tsaka da aiki a kamfaninsu mai suna Capital Gazette dake garin Annapolis na kasar Amurka, kamar yadda gidan talabijin na Channels ta ruwaito.

Wani dan jarida Phil Davis dake aiki da kamfanin ya bayyana a shafinsa na Tuwita cewa; “Dan bindiga ya bude wuta daga waje ta cikin kofofin gilasai akan ma’aikatanmu dayawa, wannan abu ne mai matukar firgitarwa.

KU KARANTA: Zargin kashe Mijinta: Shari’ar Maryam Sanda ta samu tasgaro a babbar Kotun Abuja

Shi kuwa shugaban Yansandan yankin, Bill Kramf ya bayyana cewa “Akwai mutum biyar da na san sun mutu, da dama kuma sun samu munanan rauni.” Haka zalika wani daga cikin shuwagabannin yankin Steve Schuhn ya kara da cewa an kama wanda ake zargi.

Shima Kaakakin Yansandan yankin,Ryan Frashure yace suna ta kokarin bincike a tsakanin inda aka kai harin don tabbatar da sun kama duk masu hannu cikin harin, tare da bincike kamfanin jaridar gaba daya, don kawar da duk wani Bom idan har akwai.

Daga karshe shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana alhininsa da faruwar lamarin, inda yace: “Ina jajanta ma iyalan wadanda harbe harben ya rutsa dasu, ina mika godiyata ga dukkanin wadanda suka kai musu agajin gaggawa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel